NDLEA ta kama wata mata kan hanyarta ta zuwa Qatar da  ganyen tabar wiwi

Jami’an hukumar NDLEA dake yaÆ™i da hana sha da kuma fataucin miyagun Æ™wayoyi sun tsare wata mata Æ´ar shekara 35 mai suna, Chidimma Okene.

An tsare matar ne bayan da aka kama ta tana ƙoƙarin safarar ƙunshi 20 na ganyen tabar wiwi mai nauyin 10.70Kg da aka ɓoye cikin abincin ƙabilar Igbo da ake kira Abacha da kuma busassun kayan lambu lokacin da take hanyar zuwa garin Doha dake ƙasar Qatar ta filin jirgin Saman Murtala Muhammad dake Lagos.

Hukumar ta ce jami’anta da haÉ—in gwiwar jami’an hukumar DSS ne suka samu nasarar kama matar lokacin da ake tantance fasinjojin da suke shirin hawa jirgi.

Mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ya ce Chidimma tana zaune ne a ƙasar Qatar kuma ta dawo gida Najeriya domin yin bikin Kirsimeti.

Chidimma ta ce an ajiye ta ne a  Club Dice Hotel dake yankin Ikotun a jihar Lagos inda anan ne aka bata ganyen tabar wiwin domin tayi safarar ta.

More News

Mutane 11 Sun Mutu A Wani Hatsarin Mota A Kano

Mutanen da basu gaza 11 ne ba aka tabbatar da sun mutu a yayin da wasu 16 suka jikkata mutum É—aya kuma ya tsira...

Ƙasar Amurika ta fara shirin kwashe sojojinta daga Nijar

Gwamnatin kasar Amurka ta fara shirin janye dakarunta daga jamhuriyar Nijar kamar yadda kafar yaÉ—a labarai ta CBS ta bada rahoto. Wani jami'in ma'aikatar wajen...

Sojoji sun kashe Æ´an ta’adda biyu tare da gano makamai a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun kashe wasu ƴan ta'adda biyu a ƙauyen Kana dake ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno. A wata sanarwa ranar Asabar...

An halaka mutane 6 a wani faÉ—a tsakanin Æ´anbindiga da Æ´anbanga

Mutane 6 ne suka rasa rayukansu a wata arangama da aka yi tsakanin ‘yan bindiga da ’yan banga da aka fi sani da ‘Yan...