NDLEA ta kama wasu maniyyata da suka yi niyar safarar hodar ibilis zuwa ƙasar Saudiyya

Hukumar NDLEA dake yaƙi da hana sha da kuma fataucin miyagun ƙwayoyi ta kama wasu maniyyata su huɗu ɗauke da wata hoda da ake kyautata zaton hodar ibilis ce.

Mutanen da aka kama sun haÉ—a da Usman Kamorudeen, Olasunkanmi Owolabi, Fatai Yekini, da kuma Ayinla Kemi.

A wata sanarwa ranar Alhamis, Femi Babafemi mai magana da yawun hukumar ta NDLEA ya ce an kama mutanen ne a ɗakin wani otal lokacin da suke haɗiye ƙunshin ƙwayar hodar ibilis ɗin gabanin tashin su zuwa ƙasar Saudiya a ranar Laraba.

“Mutane huÉ—un da ake zargi an ajiye su ne a wani otal inda aka shirya musu Æ™unshin Æ™wayar hodar ibilis guda 200 mai nauyin kilogiram 220 domin su haÉ—iye a lokacin da jami’an NDLEA suka farma É—akin,”

Sanarwar ta ƙara da cewa an gano ƙunshi 100 a kowane ɗaki inda mutane biyu za su haɗiye 100 kowannensu.

Tuni shugaban hukumar ta NDLEA, Buba Marwa ya yabawa jami’an hukumar na jihar Lagos kan kamen da suka yi.

More News

Muna aiki tukuru don kawar da aikata manyan laifuka a Najeriya—Tinubu ga Daraktan FBI

A ranar Juma’a ne shugaba Bola Tinubu ya karbi bakuncin daraktan hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka (FBI), Christopher Asher Wray, inda ya...

Sojojin sun kama wani mai safarar bindigogi a jihar Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin  samar da  tsaro a jihar Filato sun ka ma wani mai safarar  bindiga da ake nema ruwa...

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da matafiya akan hanyar Abuja-Kaduna

Fasinjoji da dama ne aka bada rahoton an yi garkuwa da su bayan da ƴan fashin daji suka buɗe kan wata mota ƙirar bus...

Kotu ta yanke wa É—ansanda hukuncin kisa saboda laifin kisan kai

Wata babbar kotun jihar Delta dake zamanta a Asaba a ranar Talata ta yanke wa Sufeta Ubi Ebri na rundunar ‘yan sandan Najeriya hukuncin...