
Hukumar NDLEA dake yaki da sha da hana fataucin miyagun kwayoyi ta kama wasu makafi uku dake gudanar da kasuwancin miyagun ƙwayoyi a tsakanin jihohin Kano da Lagos.
Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa.
“Jami’an NDLEA sun kama wasu makafi uku waɗanda suke kasuwancin miyagun ƙwayoyi a tsakanin Lagos da Kano a yayin da ɗaya makahon na huɗu har yanzu ba aka kama shi ba,” a cewar sanarwar.
“Asirinsu ya tonu ne biyo bayan kama wani makaho da ake zargi mai suna Adamu Hassan ɗan shekara 40 akan titin Gwagalada a Abuja akan hanyarsa ta zuwa Kano inda yake ɗauke da abun mayen da ake kira skunk mai nauyin kilogram 12 a ranar 28 ga watan Oktoba.”
“Binciken da aka gudanar ya nuna cewa bai ma san abun da yake cikin jakar da aka ba shi ya kai Kano ba.”
Bayan cigaba da binciken an samu nasarar kama shugaban gungun nasu, Bello Abubakar ɗan shekara 45 makaho ne wanda yake zaune a Lagos.
Shima Mukhtar Abubakar wanda yake da shekaru 59 makaho ne dake zaune a Lagos yana da mata uku da kuma ƴaƴa 14 shi ne mutum na biyu da aka kama.
Mukhtar da Bello su ne suke gudanar da kasuwancin kwayar a tare yayin da mutum na uku, Akilu Amadu mai shekaru 25 wanda shima makaho ne shi ne yake bayar da kudin gudanar da kasuwancin kuma shi ne ya bawa Adamu kunshin kwayar a tashar mota.