Hukumar NDLEA dake yaki da hana sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi ta kama wani ɗan kasuwa, Sherif Egbo mai shekaru 40 a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja lokacin da yake kokarin safarar miyagun kwayoyi.
A wata sanarwa ranar Lahadi, Femi Babafemi mai magana da yawun hukumar ya ce an kama mai laifin ne a ranar 14 ga watan Oktoba bayan da na’urar binciken jiki ta nuna cewa ya haɗiye ƙunshin ƙwayoyi.
Wanda ake zargi ya yi yunkurin hawa jirgin kamfanin Air France domin zuwa birnin Paris.
Babafemi ya kara da cewa daga nan aka ajiye wanda ake zargi a wurin hukumar da take tattara sheda inda anan ya kasayar da kunshi 93 na hodar heroine da nauyinta ya kai kilogram 2.222
A jawabin da yayi mai laifin ya ce yana aiki ne a wata gonar ƙyanƙyashe kaji dake Madrid a Spain kuma yana safarar miyagun kwayoyi, “