Nasarorin da gwamnatin Buhari ta ce ta samu a 2021

Asalin hoton, Presidency

Gwamnatin APC ta shugaba Muhammadu Buhari ta faɗi nasarorin da ta samu a 2021.

A wani taron manema labarai da ya gudanar, ministan yaɗa labarai Alhaji Lai Mohammed ya ce gwamnatin Buhari ta samu nasara a fannoni da dama duk da an fuskanci ƙalubale na tsaro da ta tattalin arziki a shekarar 2021.

“A shekara mai ƙarewa, babban ƙalubale shi ne na tsaro. Amma duk da wannan da kuma ƙalubalen tattalin arziki da aka saba samu, wannan gwamnatin ta samu ci gaba sosai kamar yadda za mu bayyana,” in ji Lai Mohammed.

Ministan ya bayyana nasarorin gwamnatin Buhari kamar haka:

Ɓangaren tsaro ya kasance wanda aka fi fuskantar ƙalubale cikin wannan gwamnati kamar yadda ministan yaɗa labaran ya bayyana.

Amma ya ce duk da ƙalubalen, dakarun rundunar Hadin Kai da ke aiki a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya sun kashe mayaƙa 1,000 da kuma 22,000 da suka mika kansu tare da ajiye makamansu da kuma iyalansu.

Ya ce akwai mutane 2,000 farar hula da aka ceto, an kwato makamai da harsasai masu matukar yawa. Jami’an tsaron sun tarwatsa wuraren hada bama-bamai na ISWAP da Boko Haram.

Karkashin dakarun rundunar Hadarin Daji da ke aiki a Arewa maso yammacin kasar, hare-haren da aka rika kai wa ta sama da kasa sun sanadin kashe ‘yan bindiga 427, an kuma kama 257, tare da ceto fararen hula 897 da kuma dabbobi 3,087.

Ya ce rundunar dakarun Whirl Punch da ke lura da wani bangare na jihar Kaduna sun yi nasu, sun kashe kimanin ‘yan bindiga 215 sun kama 133 tare da ceto fararen hula 296 sai kuma dabbobi 136 da aka samu a gefe guda.

Kazalika dakarun Thunder Strike da suma suke aiki a kan titin Kaduna zuwa Abuja sun kashe ‘yan bindiga 36 sun kuma kama 74 sai fararen hula 296 da aka ceto da kuma dabbobi 136 da aka kwato.

A Arewa ta Tsakiya hare-haren da rundunar dakarun Safe Haven ta kai, ta kashe manyan masu laifin 91 tare da kama wadanda ake zargi 155.

Sannan gwamnatin ta ce an ceto fararen hula 159, an samu kwato dabbobi 3,259.

Ita ma rundunar Whirl Stroke ta kashe masu laifi 158, sun kuma kama wadanda ake zargi 151 yayin da aka ceto 183.

Dakarun da ke aiki a Kudu maso Kudancin Najeriya da ake kira Delta Safe sun lalata matatun mai da aka gina ba bisa ka’ida ba 1,520 an kuma kwace kayan ajiye man da ake tatowa 5,315 tare da jiragen ruwa 617 da dai wasu sauran kayayyaki.

Bugu da kari ministan ya ce an kama litar kananzir 74,297,425 da litar danyen mai 41,971,693 da kuma litar man fetur 88,350.

An kwato motoci 174 da masu ajiyar mai 775 an kwato makamai 153.

Asalin hoton, Other

Bayanan hoto,
Lai Mohammed ya ce gwamnatin Buhari ta samu nasara duk da ƙalubalen tsaro da tattalin arziki

Cikin bayanansa, ya fara da cewa kowa ya san yadda aka fuskanci matsalar tattalin arziki tun daga 2020 kuma hakan ya shafi 2021 sanadin annobar korona, dan haka Najeriya ba ta zama ta daban ba.

Wannan matsala ta shafi tattalin arzikin Najeriya ta bangaren ci gaba a kasuwancin kayan da ake fitarwa da wadanda ake shiga da su kasar bangaren noma da sauransu.

Ya ce a watannin ukun farko na 2021 an dan samu habbakar tattalin arziki da kaso 0.51 a bangaren arzikin da ake samu a cikin gida, a watanni uku na biyu arzikin ya yi sama da kaso 5.01 yayan da kaso 4.03 ya karu a watanni ukun tsakiya.

Lai Mohammed ya ce wannan ba karamar nasara ba ce a bangaren tattalin arzikin Najeriya idan aka kwatanta da koma bayan da aka samu a 2020.

A bangaren mai babbar nasarar da aka samu, a cewar ministan ita ce ta dokar man fetur ta PIA da ta bayar da damar mayar da kamfanin hakar mai na kasar NNPC na kasuwanci wanda kowa zai iya zuba jari a cikinsa.

Ya ce ana bayyana wannan nasara a matsayin gagarumin abin da aka cimma a bangaren man fetur da gas cikin shekaru 20.

Nasara ta biyu da aka samu, a cewarsa ita ce sanar da cin ribar naira biliyan 287 da kamfanin ya samu bayan biyan haraji, irinta ta farko da aka samu cikin shekaru 44 da samar da kamfanin.

Ayyukan raya kasa

Duk da matsalar tattalin arzikn da aka samu hakan bai hana gwanatin Buhari ta yi ayyukan raya kasa ba Lai Muhammed.

Lai Mohammed ya ce ma’aikatar ayyuka da gidaje ta kasar ta samar da ayyuka masu yawa da suka hada gina titina da gidaje a 2021 a wurare daban-daban:

  • Titin Nnewi-Uduma kashi na daya da na biyu mai kisan kilomita a jihohin Enugu da Ebonyi
  • Titin Kano zuwa Maiduguri kashi na biyu mai nisan kilomita 100.08, sai kuma Shuwarin zuwa Azare a jihohin Jigawa da Bauchi.
  • Titin Kano zuwa Maiduguri kashi na uku daga Azare zuwa Potiskum mai tsayin kilomita 106.34 a jihohin Bauchi zuwa Yobe
  • Titin Vandeikya-Obudu Cattle Ranch kashi na daya na biyu a jihohin Benue da Cross River
  • Titin Sokoto zuwa Tambuwal zuwa Jega zuwa Kontagora zuwa Makera kilomita 304

Akwai bangaren manyan hanyoyi da gadoji da suma ake ci gaba da ginawa wadanda wasu an kammala wasu ana kan yi, in ji shi.

Ya ce akwai aikin gadar Naija ta biyu wadda gwamnatin tace an ci kusan kashi 70 na aikin, kuma ana sa ran kammalawa a watan Nuwambar 2022.

Sai gadar Oko Amakun da titin Atani sai kuma titin da yake sauyawa mutanen hanya da ke Onitsha-Owerri.

Sufuri

Lai Mohammed ya ce babbar nasarar gwamnatinsu shi ne ƙaddamar da sufurin aikin jirgin kasa da Muhammadu Buhari ya yi a watan Yunin 2021 wanda zai taso daga Lagos zuwa Ibadan.

Samar da layin dogo daga Kano zuwa Kaduna a watan Juyin 2021, da shirin samar da layin dogo na Lagos zuwa Kano, akwai kuma shirin layin dogo da za a yi daga Kano zuwa Maradi wanda aka bai wa Portugal aikin gina shi.

Ayyukan tallafi

Gwamnatin Najeriya ta ci gaba da fadada taimakon da take bai wa ‘yan kasar ta hanyar shirye-shirye masu yawa.

Ta fadada harkar N-Power daga mutum 500,000 zuwa miliyan 1, wadanda za su ci gaba da amfana da shirin.

Aikin ciyar da ‘yan makaranta wanda gwamnatin ta ce tana so yara miliyan 25 ne za su ci moriyarsa nan da 2030.

(BBC Hausa)

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...