Nan gaba kaɗan zamu bayyana sunayen wasu manyan mutane dake da hannu a satar mai – Garba Shehu

Mai taimakawa shugaban kasa, Muhammad Buhari kan kafofin yada labarai, Mallam Garba Shehu ya ce nan bada jimawa gwamnatin tarayya za ta bayyana sunayen wasu manyan mutane dake da hannu a satan man ƙasar nan

Shehu ya ce a wani ɓangare na kawar da zagon kasa ga tattalin arzikin ƙasar nan da wasu mutanen ƙalilan masu haɗama suke yi jami’an tsaro sun kai farmaki kan wasu wurare da ake satar danyen mai.

Garba Shehu ya bayyana haka ne a cikin shirin Politics Today na gidan talabijin Trust TV ya kuma haskaka cewa akwai wasu jami’an tsaro da suke aikata wannan haramtaccen aiki.

Ya kara da cewa ana cigaba da daukar karin sababbin matakai domin shawo kan lamarin.

More from this stream

Recomended