Nan bada jimawa za a kawo karshen rashin wutar lantarki a Kebbi

Gwamnatin jihar Kebbi ta roki mazauna jihar da su kara hakuri inda ta ce rashin wutar lantarki da ake fuskanta a jihar zai zo karshe nan bada jimawa.

A ranar 14 ga watan Satumba gobara ta kama a tashar wutar lantarki inda ta kone babbar na’urar taransifoma 330KV mallakin kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO dake birnin Kebbi.

Gobarar ta jefa jihohin Sokoto, Kebbi da kuma wasu sassan jihar Zamafara a cikin duhu.

Yakubu Bala Tafida sakataren gwamnatin jihar, shi ne ya bada tabbacin a ranar Asabar lokacin da ya ziyarci karamar tashar wutar lantarki ta hukumar TCN dake birnin Kebbi.

Sakataren ya ce ya ziyarci wurin ne a madadin gwamnan jihar wanda ya umarce shi ya saka ido akan aikin “saboda baya son al’ummarsa su cigaba da zama cikin duhu.”

Ya bayyana gamsuwarsa da aikin da aka yi kawo yanzu a kokarin dawo da wutar lantarki jihar.

More News

An sake gano gawar wani shugaban Fulani da ya ɓata a jihar Filato

An gano gawar wani Arɗon Fulani, Umar Ibrahim da ya ɓace a cikin wata rijiya dake kauyen Jokom a ƙaramar hukumar Mangu ta...

An kama Æ´an kungiyar IPOB 18 da ake zargi da kisan Æ´an sanda

Rundunar yan sandan jihar Imo ta kama mutane 18 da ake zargi da zama yan kungiyar IPOB da suke da hannu a kisan Æ´an...

Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da zaɓen gwamnan jihar Sokoto

Kotun ɗaukaka ƙara dake Abuja ta tabbatar da zaɓen, Ahmed Aliyu a matsayin gwamnan jihar Sokoto. Rukunin alkalan kotun su uku sun yi watsi da...

Kotun ɗaukaka ta soke zaɓen shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna

Kotun ɗaukaka ƙara dake Abuja, ta soke zaɓen kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Liman. Alkalan kotun uku sun bayar da umarni da a sake...