Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya kafa wani kwamitin kwararru mai mambobi 11 kan sake gina babban masallacin Juma’a na Zaria da ya rushe.
A wata sanarwa da Abdullahi Aliyu Kwarbai mai magana da yawun masarautar ya ce tsohon mataimakin shugaban kasa kuma Sardaunan Zazzau, Arc Namadi Sambo shi ne zai kasance shugaban kwamitin a yayin da Arch. Ibrahim Waziri zai zamo sakataren kwamitin.
Sanarwar ta kara da cewa “mambobin kwamitin sun haɗa da Arch. Abubakar Abdulkadir, Professor Kabir Bala, Vice Chancellor, ABU, Arch. Muhammadu Aminu Idris, Sheikh Dr. Hayatuddeen, Arch. Gambo Hamza da TPL Bello Nuhu Yakubu.
“Sauran su ne Bld. Lawal Magaji, Arch. Isa A. A and Arch. Haruna Abubakar Bamalli.”
Idan za a iya tunawa a ranar Juma’a 11 ga watan Agusta na shekerar 2023 wani sashe babban masallacin Juma’a na masarautar Zazzau ya ruguzo kan masallata.