VOA Hausa—
Da yake yiwa shugaban majalisar dattawa bayani game da shirin, ministan lafiya Osagie Ehanire yace a shirye gwamnatin tarayya take domin ceto ‘yan Najeriya, duba da cewa an shiga zagaye na biyu na annobar korona.
shugaban-faransa-emmanuel-macron-ya-kamu-da-annobar-covid
birtaniya-ba-za-ta-ci-gaba-da-zama-fursunan-covid-19-ba—johnson
najeriya-an-sami-mutum-na-farko-da-ya-rasu-sakamakon-coronavirus
Mai sharhi kan lamuran yau da kullum Bashir Baba yace wannan wani salo ne na kamfatar dukiyar talaka a yayin da matsalar tsaro ke addabar kasar.
Da yake tsokaci kan lamarin Aliyu Shamaki yace tunda annobar cutar korona ta shiga ake fitar da makudan kudaden don yaki da cutar amma har yanzu ‘yan Najeriya basu gani a kasa ba.
A nasa bangaren masanin kimiyar siyasar tattalin arziki a jami’ar Abuja Dr. Farouq Bibim Farouq yace duk da lamarin yana da kyau amma kudin yayiwa irin kasashe masu tasowa kamar Najeriya nauyi.
Yanzu dai za’a jira aga yadda lamarin zai kasance lokacin da mutane suka fara sabawa da barazanar annobar.