Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan Yuni mai zuwa.

Dangote ya bayyana haka ne a wurin taron shugabannin kamfanoni da ake gudanarwa duk shekara a Kigali babban birnin Ruwanda.

Ya ce Najeriya za ta kawo ƙarsehn shigar da mai ƙasar a cikin watan Yuni lokacin da matatar mai ta Dangote za ta fara samar da tataccen man fetur.

“A yanzu haka Najeriya bata da dalili kowane irin na shigo da  mai fa ce man fetur nan da wani lokaci cikin watan Yuni nan da wasu sati huÉ—u ko biyar Najeriya bai kamata ta shigo da man fetur ba koda lita É—aya ce,” ya ce.

Dangote ya ce za a shawo kan ƙarancin da ake samu na man fetur bama a Najeriya ba har da yammacin Afirka baki ɗaya.

Ya ce kawo yanzu suna samar da wadataccen man Diesel da yake isar Najeriya.

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya Æ™irÆ™iri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a Æ™ara wa Æ´an bautar Æ™asa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...