Najeriya ta nemi taimakon Jamus don yaĆ™i da ta’addanci

A ranar Lahadi ne shugaba Bola Tinubu ya nemi goyon bayan shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz kan yaki da ta’addanci a Najeriya.

Mista Tinubu ya miƙa wannan bukata ne a wata ganawa da ya yi da shugaban gwamnatin Jamus a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Lahadi.

“Muna yaki da ta’addanci kuma hakan yana inganta. Har yanzu muna buƙatar ƙarin tallafi a wannan yanki. Kuma don mu sami damar dorewar dimokuradiyya, bin doka da ’yanci ga jama’armu, muna bukatar mu yi gwagwarmayar tabbatar da dimokuradiyya.

“Kuma dole ne dimokuradiyya ta yi nasara a kowane lokaci domin mu cimma burinmu a Afirka. Shi ya sa ziyararku a wannan karon ta fi zama dole.

“Za ku lura, ba na buĆ™atar yin magana game da matsalolin daban-daban da ke faruwa a yankin Sahel na Afirka. Kun ga kuma kun lura da juyin mulkin da aka yi a Guinea da kwanan nan a Jamhuriyar Nijar,” in ji Tinubu

Najeriya dai na fama da matsaloli iri-iri tun bayan bayan dawowarta ta farkon dimokuraÉ—iyya.

More News

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...

Wasu É—aliban Jami’ar Jihar Nasarawa sun mutu a lokacin turmutsutsin karÉ“ar tallafin abinci

Dalibai biyu daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya barke a lokacin da suke kokarin...

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...

Miyetti Allah ta nemi a cafke Sunday Igboho saboda barazanar yaƙar Fulani

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, ta yi kira da a damke wani dan kabilar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi...