Najeriya na fuskantar mummunan matsin tattalin arziki da ba ta taɓa fuskanta ba—Sanata Abdullahi

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan tsare-tsare da harkokin tattalin arziki, Yahaya Abdullahi, ya ce Najeriya na fuskantar matsalar tattalin arziki mafi muni a tarihin wanzuwarta.

Abdullahi, wanda ke wakiltar mazabar Kebbi ta Kudu a jihar Kebbi, ya bayyana hakan ne a taron kaddamar da kwamitin majalisar a ranar Laraba.

Wannan dai kamar yadda ya ce akwai bukatar majalisar ta yi mu’amala da bangaren zartarwa a wani yunkuri na sake farfado da tattalin arzikin kasar da kuma dawo da shi kan turba.

Abdullahi ya kuma bukaci kwamitocin tsare-tsare na kasa a cikin majalisar da majalisar dattawa da su yi duk mai yiwuwa a cikin shekaru hudu don cimma burin da aka tsara na juya tattalin arzikin kasar, tare da ba da shawara ga hukuma.

More from this stream

Recomended