VOA Hausa—
Hakan na zuwa ne bayan da majalisar dokokin kasar ta Knesset ta kada kuri’ar amincewa da gwamnatin hadakar.
Netanyahu shi ne Firai Ministan da ya fi dadewa akan wannan mukami, inda ya kwashe shekara 12.
Jam’iyyu takwas ne suka dunkule wuri guda don kafa sabuwar gwamnati.
Wannan gwamnatin hadaka ta kawo karshen rashin tsayayyiyar gwamnati da kasar ta Isra’ila ba ta da ita, abin da ya sa aka yi zabuka har hudu cikin shekara biyu kafin a kai da kafa wannan gwamnatin hadaka.
Sabuwar gwammnatin Bennet mai ra’ayin mazan jiya, wanda dan jam’iyyar Yamina ne, za ta yi wa’adin shekara biyu.
Zai kuma mika wa Yair Lapid, shugaban masu matsakaicin ra’ayi na Yesh Atid, don ya karasa sauran shekara biyu.
Masu shari na hangen baya ga shan kaye da ya yi, Netanyahu na kuma fuskantar tuhume-tuhume kan zargin cin hanci da rashawa.