NAFDAC ta gargadi masu sayar da daslarsrrun kayan masarufi

Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta yi kira ga masu sayar da kayan nama daskararre da su daina sayarwa da rarraba kayayyakin da babu rajista ko kuma waɗanda aka hana shigowa da su ƙasar.

Hukumar ta bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wani taron wayar da kai na kwana ɗaya da aka gudanar a kasuwar kifaye ta Kado da ke birnin tarayya Abuja.

Shugabar hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta bayyana cewa dole ne a dakatar da shigo da haramtattun kayayyaki domin tallafa wa manoma da masu sarrafa kayan nama na cikin gida.

Adeyeye, wadda ta samu wakilcin Daraktan Hukumar reshen birnin tarayya, Mista Kenneth Azikiwe, ta sake jaddada kudurin NAFDAC na kawar da samarwa, rarraba, da kuma sayar da kayan abinci da ruwa da ba a yi wa rajista ba.

Ta kuma bayyana cewa wannan yunkuri na hukumar ya zama dole domin kare lafiyar jama’a, musamman a lokacin bukukuwan karshen shekara.

More from this stream

Recomended