Na ji kunya kan kai ni kotu da Ali Nuhu ya yi – Adam Zango | BBC Hausa

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Adam Zango ya yi karin bayani akan rikicinsa da Ali Nuhu

Kuna iya kallon bidiyon hirar da BBC ta yi da shi ta hanyar latsa hoton sama.

Fitaccen jarumin fina-finan Hausan nan Adam Zango ya ce ya ji matukar kunya da mutumin da yake kira ubangidansa a masana’antarsu wato Ali Nuhu ya kai shi kara kotu.

Adamu ya ce bai taba tsammanin cewa wani a masana’antar zai iya kai shi kotu balle Ali.

“Ai muna da shugabanni, na yi tsammanin komai ya faru su za a gayawa su sasanta, amma sai aka kai kotu, gaskiya abin ya ban kunya,” in ji Adamu.

A kwanakin baya ne dai jarumi Adam Zango ya wallafa wani sako inda ya yi ikirarin cewa tun da Ali ya sa aka zagi mahaifiyarsa shi ma sai ya rama.

Daga bisani ne Ali ya kai Adamu kotu, inda har aka aike wa Zangon sammaci.

Duk da yake a yanzu an sasanta jaruman biyu, sai dai ba dai wannan ne karo na farko da suka taba rikici har aka sasanta su ba, amma dai ba a taba batun zuwa kotu ba sai wannan karon.

Sai dai duk wannan rikici da ke faruwa tsakaninsu, a duk lokacin da BBC ta tuntubi Ali Nuhu ba ya cewa komai.

Ko a rigimar zuwa kotun ma, an tuntube shi kuma ya ce ba zai tofa komai ba sai dai a ji ranar zaman kotun.

A hirar tasa da Nasidi Adamu Yahaya kan batun kai masa sammacin, Adam ya kara da cewa: “Da na yi rubutu na zagi Ali ba alfahari nake da hakan ba, na san ba daidai ba ne.

“Sai dai daga bisani na fahimci abin da na yi ban kyauta ba, da nemansa na yi gaba da gaba na gaya masa maimakon shaida wa duniya.

“Amma na yi hakan ne saboda wadanda suka zage ni a dalilinsa su ma sun yada ne duniya ta gani.”

Daga bisani dai an sasanta jaruman biyu da suka kasance na kut da kut a da.

“Amma daga baya manyanmu sun zaunar da mu sun sasanta mu, kuma na ba shi hakuri.

“Sai dai kamar yadda aka sa na ba shi hakurin nan, ai ya kamata shi ma a kalla ya sa yaransa masu zagina su ba ni hakuri ko da sau daya ne,” in ji Zango.

Habaici

Hakkin mallakar hoto
Facebook

A cikin hirar an kuma tabo Adamu kan dalilin da ya sa yake yawan yi wa makiyansa habaici a shafukan sada zumunta, sai ya ce yawan makiyan da yake da su ne ya sa yake yawan wallafa sakon habaice-habaice a shafinsa na Instagram.

Jarumin ya ce abin da ya dauka makiyi shi ne duk mutumin da ba ya bukatar ya ga “ci gabanka ko kuma idan ka yi wani abin burgewa, amma shi bai ga hakan ba, to makiyinka ne.”

“Ko kuma mutumin da idan wani abu ya zo maka na karuwa kamar karramawa ko taron kalankuwa ko na biki, amma sai ya ce kar a bai wa wane, gara a bai wa wane, to makiyinka ne.

“Dole ne a masana’antarmu sai ka samu makiya, wasu na jikinka ne, ko daraktoci, ko jarumai ko furoduoshi ko ‘yan wasa.

“Dan Adam bai son kishiya, duk wanda ya ga wani yana daga wa ko yana neman ya wuce shi a daukaka to zai ji haushi,” a cewar Adamu.

Jarumin ya ci gaba da cewa idan ya yi maganar makiya to ba da mutum daya ko biyu yake ba, yana magana ne kan mutane da dama da suke nuna masa irin wadancan halayyar da ya ambata.

Wanda ya tsargu da shi ake

Hakkin mallakar hoto
Facebook

Jarumin ya ce idan mutum ya yi habaici to duk wanda ya tsargu, tabbas yana cikin wadanda ya rubuta sakon saboda su.

“Sannan akwai masu bin mu wato fans, amma kuma makiya ne.

Za ka yi abin da ba wanda ya taba yi a duniya, amma sai su ce karya ne kwaikwayon wani ka yi.

“Don haka na kan yi wasu abubuwan ne don na burge masoyana, a hannu guda kuma na aikewa makiyana sako a fakaice cewa na san irin kiyayyar da suke min,” in ji Adamu Zango.

Rayuwar Adam A Zano a takaice

Hakkin mallakar hoto
Adam Zango

  • An haife shi a garin Zangon Kataf a jihar Kaduna
  • Ya bar garin a 1992 bayan rikicin kabilancin da aka yi
  • Ya koma arayuwa a jihar Plateau inda ya yi karatun Firamare
  • Talauci ya hana shi ci gaba da karatu a wancan lokacin
  • Tun yana yaro ake masa lakabi da Usher – mawakin nan dan Amurka saboda yadda yake rawa
  • Ya koma Kano inda ya fara aiki a wani kamfanin kade-kade da raye-raye
  • Fim dinsa na farko shi ne Sirfani, wanda ya ce shi ya shirya shi da kansa
  • Ya fito a fim sama da 100 a tsawon shekara 16

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 6 da ake zargi da kisan kai da fashi da makami a Gombe

Rundunar ƴan sandan jihar Gombe ta ce a cikin mako guda  jami'an ta sun kama wasu mutane 6 da ake zargi da aikata fashi...

Ƴan sanda sun kama wani fursuna da ya tsere daga gidan Gyaran Hali na Maiduguri

Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta ce jami'an ta sun kama Kyari Kur ɗaya daga cikin ɗaurarrun da suka tsere daga gidan gyaran hali ...

Ƴansanda sun kama mutumin da yake lalata da ƴar cikinsa

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun kama Ibrahim Aliu mai shekaru 41 a duniya a Papa Olosun, Oja Odan a karamar hukumar Yewa...

Majalisar wakilai za ta samar da jami’ar Bola Ahmad Tinubu

Ƙudurin kafa dokar kafa Jami'ar Karatun Yaruka Ta Bola Ahmad Tinubu ya tsallake karatun farko a majalisar wakilai ta tarayya. Mataimakin shugaban majalisar, Benjamin Kalu...