
Mutum guda ya jikkata a ranar Asabar lokacin da wata babbar mota dake dauke da kayan dab’i ta faɗa cikin wani rami bayan da ta fado daga kan gadar Oshodi a birnin Lagos.
An ruwaito cewa birki ya kwace wa motar a lokacin da ta ke saukowa daga gadar ta Oshodi bayan da ta fito daga hanyar Oshodi-Oke zuwa mile 2.
A wata sanarwa da aka fitar, Adebayo Taofiq mai magana da yawun hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Lagos, LASTMA ya ce an ceto wanda ya jikkata aka kuma garzaya da shi ya zuwa asibitin dake kusa domin samun kulawar likitoci.
Taofiq ya ce an kama direban motar an mika shi hannun jami’an yan sanda na caji ofis din Makinde domin fadada bincike tare da gano dalilin shanyewar birkin motar.

