Mutum na farko da aka dasawa ƙodar Alade ya fito daga asibiti kusan makonni uku kenan da yi masa aikin tiyata
A ranar 16 ga watan Maris likitoci a babban Asibitin Massachusetts dake ƙasar Amurika suka sakawa Richard Slayman mai shekaru 62 ƙodar alade wanda ya zama mutum na farko da aka fara yi wa irin haka.
Asibitin ya ce ƙodar alade da aka sauya ƙwayoyin halittar ta wato DNA a turance ita aka yi amfani da ita wajen sakawa mutumin a wani aikin tiyata da ya ɗauki tsawon sa’o’i 4.
Slayman ya jima yana fama da cutar ciwon suga da kuma hawan jini a tsawon shekaru
Ya shafe shekaru da dama ana masa wankin ƙoda kafin ya samu ayi masa dashen ƙoda ta wani wanda ya mutu a shekarar 2018.
Ƙodar ta fara gazawa bayan shekaru 5 da aikin inda hakan ya tilasta masa cigaba da wanke ƙods