Mutum 12 Sun Halaka A Fadan Kabilanci A Taraba

SP Abdullhi Usman kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Taraba ya tabbatar mana da cewa ‘yan bangan da ake zargin sun ware kansu ne suka tafi yin wannan aikin ba tare da sanin hukumar ‘yan sandn Jihar ba.

Ya kara da cewa yanzu haka rundunar ‘yan sandar Jihar ta aika da dakaru domin kamo wadanda ake zargin.

Kuma tuni sun samu nasarar kamo wasu biyu daga cikin wadanda ake zargin da aikata wannan mummunar kisan.

Mode Muhammad mai anguwar Zudai shima ya tabbatar mana da cewa ‘yan bangan sun kashe mutane goma sha biyu nan take a gaban sa kuma suka ce sai sauran sun bar rugar gaba daya.

Malan shehu Aliyu mahaifin wani yaron da aka kashe, ya bukaci gwamnatin Jihar da na tarayyyar Najeriya da su musu adalci akan wannan irin kisan gilla akan su ba dare barana a Jihar Taraba.

‘Yan Banga Sun Kashe Mutane Sama Da 12 A Yankin Zudai, Karamar Hukumar Bali Na Jihar Taraba
‘Yan Banga Sun Kashe Mutane Sama Da 12 A Yankin Zudai, Karamar Hukumar Bali Na Jihar Taraba

Alhaji Adamu Zubai dagacen Zudai ya ce yanzu haka dai ‘yan bangan suna nan cikin daji, sai abin da Allah yayi kan kawo karshen mastalar rashin tsaron da ya addabi yakin nasu.

A nasu bangaren kungiyar Sullubawa dake Jihar atabakin Alhaji Ardo Kiri, Ardon Sullubawa mazaunan yankin Bali da Gossol a Jihar Taraba, shi bai dauki wadannan a matsayin ‘yan banga ba ya daukesu tamkar ‘yan ta’addan ne wadanda aka dauki hayarsu domin kwace iko a Jihar.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...