Mutanen Sokoto na ta murnar kashe ƙasurgumin ɗanbindigar nan Halilu Buzu

Mazauna yankin Sokoto da kewaye na murnar kashe wani kasurgumin shugaban ‘yan bindiga, Kachallah Halilu Buzu, da sojojin Najeriya suka yi a farmakin da suka kai a jihar Zamfara.

Mummunan farmakin da sojoji suka kaddamar a maboyar ‘yan bindigar a Zamfara a ranar Alhamis, ya yi sanadin kashe ‘yan bindiga da dama ciki har da Kachallah Halilu Buzu. 

Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro (CDS), Janar Christopher Musa, ne ya tabbatar da kashe wadannan ‘yan bindigar da suka yi kaurin suna wajen kai hare-hare kan ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a fadin kasar nan.

CDS Musa ya ce dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar kawar da wani sarkin ‘yan ta’adda, wanda aka fi sani da Halilu Buzu tare da wani adadi mai yawa na mayakansa a kauyen Mayanchi da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara a ziyarar da ya kai wa gwamnan jihar a ranar Juma’a.

Shahararren madugun ‘yan fashin, wanda aka fi sani da Kachallah ko Halilu Buzu, dan kasar Nijar, ba wai kawai yana ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma ba ne, har ma makamai da harsasai yake samarwa ga kungiyoyin ‘yan fashi da dama.

Kachalla, wanda ke da alaka mai karfi wajen safarar makamai zuwa Najeriya, ya kuma kasance mai ba da jagoranci ga shugabannin kungiyoyin ‘yan fashi da dama irin su Bello Turji da makamantansu.

More News

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...

Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake...

AMBALIYA: Bafarawa ya ba wa al’ummar Sokoto gudunmawar naira biliyan 1

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya bayar da gudummawar Naira biliyan daya ga al’ummar Sokoto, domin rage radadin wannan annoba.An bayyana hakan...

Ƴanbindiga sun kai hari coci-coci a Kaduna, sun kuma yi garkuwa da mutane

Mutane 3 ne ake fargabar sun mutu, sannan an yi garkuwa da wasu 30 bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a...