Mutanen da suka fito daga mazaɓar dakataccen dan majalisar dattawa, Sanata Abdul Ningi sun shigar da ƙara a gaban babban kotun tarayya dake Abuja inda suka nemi kotun da ta soke dakatarwar da aka yi masa.
Wasu daga cikin mutanen mazaɓar ne suka shigar da ƙarar a ranar Laraba masu shigar da ƙara da suka haɗa da Sadiq Abubakar, Abdullahi Jibrin, Adamu Hassan, Shafiu Abdullahi, Magaji Shafihu, William John, Yahaya Saleh, Yusuf Adamu, Adamu Sulaiman, da kuma Habibu Mamuda sun fito ne daga mazaɓar Dan Majalisar Dattawa Ta Bauchi Ta Tsakiya.
Suna ƙarar Majalisar Dattawan Najeriya, shugaban majalisar dattawan, Godswill Akpabio, Sanata Olamilekan Adeola, akawun majalisar ƙasa, akawun majalisar dattawa da kuma dogarin majalisar.
A cikin ƙarar lauyan masu ƙara, Rueben Egwuaba ya ce mutanen mazaɓar na buƙatar kotun ta bayar da umarnin mayar da Abdul Ningi muƙaminsa na Sanata mai wakiltar mazaɓar Bauchi Ta Tsakiya tare da dukkanin hakki da damarmaki dake tattare da muƙamin nasa.
Sun kuma buƙaci kotun ta hana waɗanda ake ƙara yin duk wani abu da zai hana mai ƙara gudanar da aikinsa na ɗan majalisar dattawa.