Mutane Sama Da 30 Sun Rasa Rayukansu Bayan Da Kwale Kwalensu Ya Kife

A Najeriya rahotanni daga jihar Bauchi na hadarin jirgin daya faru a karamar hukumar Kirfi, na nuni da cewa ana kyautata zaton mutane sama da 30 ne suka mutu, kokuma sun bace a sanadiyar kifewar jirgin ruwa da yake dauke da mutanen kauyukan dake yankin karamar hukumar wanda yawancinsu manoma ne.

More from this stream

Recomended