
Ana fargabar mutuwar mutane da dama bayan da wani kwale-kwale ya kife a garin Gurin dake karamar hukumar Fufore ta jihar Adamawa.
Mutane da yawancinsu mata ne da kananan yara na kan hanyarsu ne ta komawa gida daga gona da kuma suna lokacin da jirgin ruwan na katako ya kife.
Sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Adamawa, Dr Muhammad Suleiman ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce lamarin ya faru da tsakar rana kuma ana cigaba da aikin ceto.
Mamba dake wakiltar mazabar Fufore/Gurin a majalisar dokokin jihar ya tabbatar da faruwar lamarin.
Hakan na zuwa ne kasa sa’o’i 48 bayan da mutane 8 suka mutu a wani hatsarin jirgin ruwa a Rugage dake karamar hukumar Yola South.