Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a karamar hukumar Kukawa ta jihar Borno ta bi ta kan wani abin fashewa da ake zargin ‘yan ta’addar ISWAP ne suka dasa.

Sahihan majiyoyin leken asiri na soji sun shaida cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 17 ga Afrilu.

Kakakin runduna ta 7, Laftanar Kanal Ajemusu Jingina, ya ce, “Ba zan yi magana a kan lamarin ba, domin wurin yana karkashin ikon rundunar hadin gwiwa ta Multi-National Joint Task Force, wadda ke da hedikwata a Ndjamena, Jamhuriyar Chadi.”

Jihar Borno dai na daga cikin jihohin da ke fama fa tashin hankali ƴan Boko Haram.

More from this stream

Recomended