Mutane da dama sun jikkata a gobarar tankar mai a Abuja

Wata tankar mai dake maƙare da fetur tayi bindiga ta kama da wuta inda ta jikkata mutane da dama tare da jefa garin wasu cikin firgici da daren ranar Litinin a yankin Maitama dake birnin tarayya Abuja.

Lamarin da ya faru akan titin Shehu Shagari ya jikkata mutane da dama cikin har da wasu fasinjoji dake cikin wata motar haya..

Wani da ya sheda faruwar lamarin ya bayyana cewa wurin ya hargitse a lokacin da abun ya faru a yayin da jami’an bada agajin gaggawa ke aikin ɗauke waɗanda suka jikkata ya zuwa Asibiti.

Wani jami’in lafiya dake Asibitin Gundumar Maitama da ya nemi a ɓoye sunansa ya tabbatar da cewa an kai wasu mutanen da suka jikkata sashen bada agajin gaggawa na asibitin.

Wasu da suka samu tsira daga wutar sun faɗawa ma’aikatan asibitin cewa direban motar ya tsere bayan  da motar ta faɗi. kafin daga bisani tayi bindiga.

More from this stream

Recomended