Mutane biyu sun ƙone sosai a wata gobarar gidan mai a Lagos

Mutane biyu ne suka ƙone sosai a yayin da wasu da dama suka jikkata a wata gobara da ta kama a wani gidan mai mallakin kamfanin Mobil a jihar Lagos.

Lamarin ya faru ne ranar Alhamis da misali ƙarfe 11: 00 na safe a gidan man dake kusa da Airport Hotel, Ikeja dake kan titin Obafemi Awolowo.

Gobarar ta samo asali daga wata motar  ɗaukar iskar gas da ta kama da wuta kana ta bazu  ya zuwa sauran sassan gidan man da maƙotan gidaje.

Nosa Okunbor  Shugaban sashen hulɗa da jama’a na hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Lagos, LASEMA ya ce musabbabin da yasa motar mai ɗaukar tan 12 na iskar gas ta kama da wuta.

Ya ce motoci 6 da suka haɗa da na gida da na haya gobarar ta rutsa da su.

More News

Jam’iyar PDP ta dakatar da Dino Melaye

Jam'iyar PDP a jihar Kogi ta dakatar da Dino Melaye tsohon ɗantakarar gwamna a jihar kan zargin cin amanar jam'iya. Shugabannin jam'iyar PDP na mazaɓar...

Sojoji sun kashe gawurtaccen ɗan bindiga Kachalla Buzu

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar kashe gawurtaccen ɗan bindiga Kachalla Halilu Sububu wanda aka fi sani da Kachalla Buzu. An kashe Kachalla ne...

Dakarun Najeriya sun hallaka ƴanbindiga a Neja

Rundunar sojin saman Najeriya ta hakala 'yanbindiga sama da 28 a yankin ƙaramar hukumar Shiroro dake jihar Neja.Wata sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai...

Tinubu ya gana da Sarki Charles

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga Sarki Charles na Birtaniya a fadar Buckingham a wata ziyara da yakai. Wannan ce ganawa...