Mutane 9 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Sokoto – AREWA News

Mutane 9 ake fargabar sun mutu bayan da kwale-kwalen da suke tafiya a ciki ya kife da su a kauyen Birjingo dake karamar hukumar Goronyo ta jihar.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa yawancin mutanen dake cikin jirgin mata ne da kananan yara da kuma wata budurwa da ake shirin yiwa aure da suke tare da mahaifiyarta.

Bayanai sun bayyana cewa jirgin na dauke da mutane sama da 30 lokacin da lamarin ya faru.

An ce fasinjojin na kan hanyarsu ne ta zuwa gonar shinkafa dake tsallaken kogin inda suke aikin kwadago.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Isa Muhammad kansilan dake wakiltar mazabar Birjingo,ya ce hatsarin ya faru ne da misalin karfe 8 na safiyar ranar Laraba.

Dagacin kauyen Birjingo, Alhaji Shehu Dangaladima ya ce jirgin ya nutse ne saboda an dauki mutane fiye da ka’ida a ciki.

More News

Ƴan bindiga sun ƙone ginin hedkwatar ƙaramar hukuma tare da kashe jami’an tsaro

Ƴan bindiga sun kai farmaki hedkwatar ƙaramar hukumar, Isiala Mbano dake jihar Imo da tsakar daren ranar 3 ga watan Satumba inda suka ƙone...

An kama wasu ƴanta’adda da ke da alaƙa da Turji

Akalla mayaka 18 da ke da alaka da fitaccen shugaban ‘yan ta’adda Bello Turji aka kama a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin...

Dakarun Najeriya sun kai farmaki wa ƴan’adda a Borno, wani kwamanda ya miƙa wuya

Rundunar sojin Najeriya ta sanar a ranar Lahadin cewa dakarunta sun yi nasarar kashe wani fitaccen kwamandan kungiyar Boko Haram, Abu Rijab da wasu...

Yadda wani adalin direba ya kawo cigiyar haka maƙare a kuɗi

Wani direban motar kasuwa ya mayarwa rundunar ‘yan sandan jihar Kano jakar da ta bata dauke da makudan kudade.  Direban mai suna Safiyanu Mohammed...