Fasinjoji 8 aka tabbatar sun mutu wasu biyu kuma suka jikkata bayan da wata motar fasinja ƙirar ta daki wata babbar mota a kusa da gonar Yakwo dake dai-dai da wani shingen binciken ababen hawa na sojoji akan hanyar Abuja zuwa Lokoja.
Wani shedar gani da ido ya ce hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 07:00 na safiyar ranar Lahadi a yayin da wata mota ƙirar Sharon mai rijistar namba BWR 662 XB da ta fito daga Lokoja wuce mota akan wata kwana nan take ta ci karo da wata babbar mota ta kamfanin BUA da ta fito daga Abuja.
Ya ce motar na É—auke da fasinjoji 11 da suka fito daga yankin kudu maso gabas zuwa Abuja.
Wani jami’in hukumar kiyaye afkuwar hatsura ta Æ™asa FRSC da ya nemi a É“oye sunansa ya tabbatar da faruwar hatsarin da kuma yawan mutanen da abun ya rutsa da su.