Hukumar NCDC dake yaki da cututtuka masu yaɗuwa ta tabbatar da cewa mutane 74 ne suka kamu da cutar zazzaɓin Lassa a makon da ya wuce.
A jihohi 9 ne aka samu karin mutanen da suka kamu da cutar mai haɗarin gaske inda jihar Ondo take kan gaba da yawan mutane.
Mutane 28 ne suka kamu da cutar a jihar Ondo sai jihar Bauchi da Edo dake da mutane 18 kowaccen su.
Sauran jihohin da aka samu bullar cutar sun hada da Oyo (3), Ebonyi(3), Benue(1),Katsina(1),Taraba(1) da kuma Kaduna(1).
Cutar zazzaɓin Lassa na hatsari sosai inda take da saurin kisan waɗanda suka kamu da ita.