Mutane 5 Sun Mutu A Ambaliyar Ruwa A Adamawa

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Adamawa ADSEMA ta ce mutanen da basu gaza 5 ne ba suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da ta shafi al’ummomi da dama na jihar.

Shugaban hukumar ta ADSEMA, Sulaiman Muhammad shi ne ya bayyana haka a yayin ganawa da manema labarai a Yola.

Muhammed ya ce gidaje da dama da kuma ababen more rayuwa ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da su a kananan hukumomin Fufore, Yola South da kuma Mubi North.

Ya ce hukumar ta na gudanar gangamin wayar da kai iri daban-daban kan ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 21 na jihar inda ya shawarci mazauna yankin da za a iya fuskantar ambaliyar ruwa da su koma inda wurare masu tudu.

More from this stream

Recomended