
Mutane 22 ne suka mutu wasu 20 kuma suka samu munanan raunuka a wani hatsarin mota da ya rutsa da motar tirela dake dauke da dabbobi akan titin Lapai-Lambata dake jihar Niger.
Aishat Saadu kwamandar hukumar kiyaye afkuwar haɗura ta kasa FRSC shiyar jihar Niger ta tabbatarwa da wakilin jaridar Daily Trust faruwar hatsarin inda ta ce motar tirelan na dauke da dabbobi da kuma mutane 42 lokacin da tayi hatsarin da misalin karfe 3:00 na dare inda mutane 20 suka mutu nan take.
Ta ce motar tirelan ta taso daga jihar Kano kuma ta nufi jihar Lagos ne lokacin da tayi hatsarin kilomita 10 kafin garin Lambata.
“Tun da farko Ina cikin masu aikin ceto saboda sun kira layin jami’an kai daukin gaggawa na hedkwatar hukumar mu. Saboda haka na shiga aikin ceton kai tsaye.Hatsarin ya yi muni sosai,” ta ce.
“Hatsarin ya rutsa da mutane 42 dukkansu maza. Mutane 22 sun mutu a wurin nan take 20 kuma suka jikkata,”
Ta kara da cewa gudun wuce sa’a ne ya jawo faruwar hatsarin.