Mutane 13 ne suka kone kurmus a wani mummunan hatsarin mota da ya faru akan hanyar Wudil zuwa Gaya a jihar Kano.
Shugaban hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa shiyar Kano, Zubairu Mato ya ce motoci biyu ne suka ci karo da juna.
A cewar sa guda daga cikin motocin kirar Hiace Hummer mai namba GML 102 TA ta kamfanin sufurin Kano Line ta fito ne daga jihar Gombe inda ta yi tawo mu gama da wata mota kirar Jeep da misalin karfe 8 na daren ranar Lahadi.
Mato ya alakanta dalilin hatsarin da gudun wuce sa’a.