Mutane 11 sun kone a hatsarin mota a Kogi

Mutane 11 ne suka kone kurmus a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a jihar Kogi.

Hatsarin da ya rutsa da motoci da dama ya ya faru ne a kusa da gadar Olofu dake Ochadamu a jihar ta Kogi.

A wata sanarwa mai magana da yawun hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa FRSC, Bisi Kazeem ya ce hatsarin ya rutsa da abin hawa 20 da suka hada da tankar mai 1, kananan motoci 12 sai kuma babura 6.

Kazeem ya ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa kwacewar birki da kuma kawo tsaiko a hanya ne musabbabin faruwar hatsarin.

More from this stream

Recomended