Mutane 10 sun mutu 7 sun jikkata bayan da wani gini ya ruguzo a Ibadan

Aƙalla mutane 10 aka bada rahoton sun mutu bayan da wani gini ya ruguzo a Ibadan babban birnin jihar Oyo.

Lamarin ya faru da tsakar daren ranar Alhamis a yankin Jegede Olunloyo dake birnin.

Wata sanarwa da hukumar kashe gobara ta jihar ta fitar ta bayyana cewa mutane 7 aka samu nasarar zaƙulowa daga cikin ɓaraguzan ginin.

Sanarwar ta ce hukumar ta samu kiran kai ɗaukin gaggawa da misalin ƙarfe 08:00 daren ranar ta Alhamis.

Ruguzowar ginin ta shiga cikin jerin ƙaruwar ruguzowar gini da ake cigaba da yawan samu a faɗin ƙasarnan.

Ko da a ranar Lahadin da ta gabata sai da mutane 7 suka mutu a wani da ruguzo a Sabon Lugbe dake Abuja.

Related Articles