Mutane 10 a wani hatsarin mota kan hanyar Lagos-Ibadan

Mutane 10 ne aka tabbatar sun mutu a wani hatsarin mota da ya faru akan hanyar Lagos zuwa Ibadan.

Ahmed Umar shugaban shiya na hukumar kiyaye afkuwar hatsura FRSC a jihar Ogun shi ne ya tabbatar da haka.

Ya ce hatsarin da ya rutsa da babban mota ƙirar Mack da kuma wata Toyota Hiace ya faru ne da misalin ƙarfe 04:30 na asuba a wajejen yankin Oniworo.

Jumullar mutane 19 ne hatsarin ya rutsa da su da suka hada da maza 13 da kuma mata 6 sai yarinya daya.

“Maza biyu sun samu raunuka a yayin da maza 7 da mata biyu da kuma wata karamar yarinya suka mutu” Ya ce.

A cewar Umar an ajiye gawarwakin a dakin ajiye gawa na Ipara wadanda suka jikkata kuma aka kai su Asibitin Victory dake Ogere.

More from this stream

Recomended