Musulmi a Zaria sun yi taron addu’o’i saboda mummunan halin matsi da Najeriya ke ciki

Musulmi a garin Zaria na jihar Kaduna, sun gudanar da addu’a ta musamman domin neman taimakon Allah kan halin da ‘yan Najeriya ke ciki a halin yanzu.

Sallar ta musamman da aka gudanar a filin Sallar Idi na Mallawa da ke Zariya ta samu halartar mata da maza daga sassa daban-daban na garin.

Da yake jagorantar addu’ar ta musamman, babban limamin masallacin Juma’a na Bakin Kasuwa (Tudun Wada), Malam Muhammadu Sani Labudda, ya bayyana wahalhalun da ake ciki a yanzu a matsayin wanda ba za a iya jurewa ba wanda ke bukatar taimakon Allah.

Ya ce halin da ake ciki a kasar nan na da matukar wahala da ke bukatar addu’o’i na gama-gari musamman ganin yadda farashin kayayyakin masarufi ke tashi a ranar da Musulmi ke gab da shiga watan Ramadan.

More from this stream

Recomended