Murja ta ƙi amincewa da tayin aurar da ita da Gwamnan Kano Abba ya yi mata

Murja Ibrahim Kunya ta bayyana cewa ba ta da sha’awar shirin auren zaurawa da za a yi a Kano wanda hukumar Hisbah ta jihar ta shirya.

Ana sa ran shirin zai laƙume kusan naira biliyan 1 wa gwamnatin jihar.

A kwanakin baya ne gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir ya fito bainar jama’a ya bayyana aniyarsa ta aurar da Murja Ibrahim, fitacciyar jarumar TikTok kuma mai goyon bayansa.

Shirin wanda tun asali gwamnatin Kwankwaso ne ta fara aiwatar da shi, daga baya kuma gwamnatin Ganduje ta dakatar da shi, gwamnatin Abba Kabir ce ta dawo da shi.

Dangane da wannan tayin, Murja ta ki amincewa, inda ta jaddada cewa goyon bayanta ga gwamnan ba wai don neman abin duniya bane.

Murja ta kara da cewa ita mabiyiya ce mai biyayya ga kungiyar Kwankwasiyya karkashin jagorancin Dr. Rabiu Kwankwaso, wadda ke goyon bayan takarar Abba ta gwamna.

More News

Gwamnatin Abia za ta fara biyan albashi mafi maranci na naira 70,000 a watan Oktoba

Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa za ta fara biyan sabon albashi mafi karanci na naira 70,000 ga ma’aikatanta daga watan Oktoba 2024.Kwamishinan...

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...

Faruk Lawan ya kammala zaman gidan yarin Kuje

An sako tsohon ɗan majalisar wakilai ta tarayya, Hon Faruk Lawan daga gidan yarin Kuje bayan da ya kammala zaman gidan yarin na shekaru...