
Wasu kungiyoyi a A jahar Kaduna da ke arewacin Najeriya, sun fara tofa albarkacin bakinsu dangane da zaben da gwamnan jihar Nasir el-Rufai, ya yi na mace a matsayin mataimakiyarsa a zaben 2019.
Wasu kungiyoyi na mata sun ce hakan ya yi masu da di kasancewar dama abin da suka dade suna fatan gani a siyasar Najeriya ke nan.
Kungiyoyin matan sun ce zabar mace a matsayin mataimakiyar gwamna a jiharsu, abin ya yi kyau kwarai da gaske saboda dama sun da de suna korafin cewa an bar mata a baya duk kuwa da irin gudunmuwar da suke bayarwa a fagen siyasar kasa.
Kungiyoyin matan suka ce wannan mataki na gwamnan ya nuna cewa ana yi da su, sannan kuma ana amfani da irin gudunmuwar da mata ke bayarwa a fagen siyasar Najeriyar.
To sai kuma duk da wasu na son barka da matakin zabar mace a matsayin mataimakiyar gwamnan jihar ta Kaduna, wasu a gefe guda na sukar matakin inda suke ganin sam bai dace ba.
Gwamna Nasir El-Rufai, ya ce ya zabi mataimakiyar ta sa Hadiza Balarabe wadda likita ce domin bai wa mata damar damawa da su a gwamnati da ma siyasar jihar ta Kaduna.
Kowacece mataimakiyar da gwamnan ya zaba?
Hakkin mallakar hoto
The Guardian Nigeria
Dr. Hadiza Balarabe ita ce babbar sakatariya a hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Kaduna.
A cewar El-Rufai, manyan ayyukan Dr. Hadiza Balarabe sun hada da kaddamar da shirye-shiryen da suka inganta tsarin kiwon lafiya na jihar ta Kaduna.
Dr. Hadiza ta soma aiki a fannin lafiya na babban birnin tarayya, Abuja a 2004 inda ta kai matsayin daraktar kula da lafiya.
Gabanin hakan, ta rike mukamin babbar rijistara a asibitin koyarwa na Jam’iar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Ta karanci aikin likita a Jami’ar Maiduguri inda ta kammala a shekarar 1988.
Wannan ne dai karo na farko a tarihin jahar Kaduna da wata babbar jam’iyya ke zaben mace a matsayin abokiyar takarar mukamin gwamna.