Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya ce gwamnatinsa ta kashe Naira miliyan 900 ga wasu dalibai marasa galihu 41 don yin karatun digiri na farko a fannin likitanci, MBBS, a jami’ar Al-Nahda da ke kasar Masar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a wajen kaddamar da tallafin karatu na kasashen waje na MBBS a Katsina.
Ya ce an zabo dalibai marasa galihu ne bisa cancanta, bayan da aka gudanar da jarrabawa ga masu sha’awar shiga makarantun gaba da sakandire na gwamnati a jihar.
A cewarsa, kudaden za su isa a biya dukkan kudaden karatunsu da sauran bukatunsu na tsawon shekaru biyu.
Ya ce gwamnatin jihar ta fara shirin bai wa daliban MBBS tallafin karatu daga kasashen waje domin magance karancin likitocin jihar.