Kungiyar Matasan Arewa mai suna Arewa Youth Consultative Forum ta yi gargadi game da halin da ƴan Najeriya da ke Sudan ke ciki.
Cikin wata takarda da kungiyar ta fitar, ta nuna damuwarta matuka game da yadda Gwamnatin Najeriya ke nuna halin-ko-in-kula wajen kwaso yan kasarta da suka tsangare a kasar Sudan saboda yakin da ake fama da shi.
Ga abin da takardar take cewa:
A matsayinmu na ‘yan Najeriya wadanda ba su ji dadin halin da ‘yan Najeriya ke ciki a Sudan ba sakamakon yaki da kashe-kashe da ake yi, muna jin ya zama wajibi mu bayyana matsayarmu ta karshe a kan wannan zubar da jini da kone-kone.
Don haka muna so mu bayyana abubuwa kamar haka:
1. Ba abin yarda ba ne cewa yayin da kasashe da dama ke kwashe ‘yan kasarsu daga Sudan, tamu ce kadai kasar Afirka da ke ba da uzuri.
2. Kasancewar dubban ’yan Najeriya mazauna Sudan musamman daliban Arewa maza da mata ne suka fi yawa, mun yi watsi da makahon uzurin da ofishin jakadancin Najeriya ya bayar a kan wahalar kwashe ‘ya’yanmu maza da mata. Babu wani dan Arewa da ke zaman lafiya a kasar nan tun da aka fara kashe-kashe da kone-kone a Sudan.
3. Muna sane da cewa gwamnatin Sudan ta riga ta yi gargadin cewa lamarin zai kara ta’azzara, ta kuma ba da wa’adin sa’o’i 72 ga kasashen da ‘yan kasar da ke gudanar da harkokin kasuwanci ko kuma makaranta a kasar da a kwashe su. Ba za mu iya fahimtar dalilin da ya sa duk abin da muke samu a halin yanzu shine uzurin ofishin jakadancinmu cewa yin hakan zai yi wahala. Me ya hana mu yin amfani da wa’adin sa’o’i 72 da farko?
4. A bayyane yake cewa a halin yanzu rayuwa ta shiga cikin hadari, musamman ga ’yan’uwanmu maza da mata na Arewa da ke karatu a Sudan, duba da yadda wannan yaki ke kara ta’azzara, wanda ya hada da amfani da muggan makamai.
5. A matsayinmu na kungiya, muna so mu bayyana sarai cewa idan aka kashe ’yan’uwanmu maza da mata na Arewa da ba su ji ba ba su gani ba a makaranta a Sudan a wannan yakin, za mu dora wa ofishin jakadancin Najeriya da ke Sudan alhaki.
6. Muna so mu jaddada cewa, ba don komai ba ne a bar wa wadannan matasa da ba su ji ba ba su gani ba a Najeriya, domin suna da kasar da ke da hakkin tsarin mulki da na shari’a na kare rayukan ‘yan kasa a duk inda suke a duniyar nan.