Mun ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutu—Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin 29 ga watan Mayun 2023 a matsayin ranar hutu a fadin kasar nan a hukumance.

Matakin dai shi ne baiwa dukkan ‘yan Najeriya damar gudanar da bikin rantsar da zababben shugaban kasar karo na 16 bisa tafarkin dimokradiyya.

Dr Shuiab Belgore, babban sakatare a ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a. Ya kara da cewa ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya.

Aregbesola ya mika sakon fatan alheri ga daukacin ‘yan Najeriya kan wannan gagarumin biki tare da yaba musu kan yadda suka yi imani da dimokuradiyya.

Wannan imanin ya bayyana a zaben da aka yi a fadin kasar wanda ya sa aka rantsar da shugaban kasa da mataimakinsa, da kuma a dukkan zabukan kasar.

Ya kuma yi kira ga kowa da kowa da ya yi amfani da wannan hutun don yin tunani a kan tafiyar dimokuradiyyar al’umma da makomarta a karkashin sabon shugabanci.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...