Hukumar Kiyaye Haɗɗura ta Ƙasa (FRSC) reshen jihar Kaduna ta ce mutane 16 ne suka mutu yayin da wasu hudu suka jikkata a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Kano zuwa Kaduna ranar Lahadi da misalin karfe 11:20 na safe.
Kwamandan shiyyar Kaduna, Kabir Nadabo, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya cewa, hatsarin ya afku ne a mahadar Taban Sani dake Tashar Yari kan hanyar Kano zuwa Kaduna.
Nadabo ya ce, “mummunan hatsarin motan ya hada da wata mota kirar Toyota Bus, mai lamba TRB 674ZG, wadda ta taso daga jihar Kano zuwa Makurdi ta jihar Benue, ya kuma bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce gona da iri da direban ya yi, wanda ya sa motar ta faɗa cikin rami.