A kalla mutane 12 ne suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a titin Baimari–Geidam a jihar Yobe.
Shugaban Sashen Hukumar Tsaro ta Tituna (FRSC) a jihar, Livinus Yilzoom, ya tabbatar da mutuwar a cikin wata sanarwa da ya fitar a Damaturu ranar Laraba.
A cewar sa, hatsarin ya faru da misalin karfe 10 na dare ranar Talata, lokacin da wata motar Howo ta hadu da wata bas mai lambar rajista BAU 124 YF kusa da garin Chelluri.
Ya bayyana cewa, matafiyan bas din 12 ne suka kone bayan motar ta tashi da wuta.