Kamar kowane mako, mukan tattaro muku wasu abubuwan da suka faru a ƙarshen mako, a wannan makon ma, mun tattaro muku muhimman abubuwan da suka faru daga 13 ga watan Satumba zuwa 19 ga watan Satumba.
El-Rufai ya rattaɓa hannu kan dokar yi wa masu fyade dandaƙa
Asalin hoton, FACEBOOK/NASIR EL-RUFAI
A ranar Larabar da ta gabata ne Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya rattaɓa hannu kan dokar hukunci mai tsanani a kan duk wanda aka kama da laifin fyade.
Dokar ta ba da damar kisa ko yin dandaƙa ga duk wanda aka kama ya yi wa ƙananan yara ‘yan ƙasa da shekara 14 fyade.
Haka ma ƙarkashin dokar, za a iya yanke musu hukuncin ɗaurin rai-da-rai.
Idan a ka kama mace kuwa dokar ta ce za a cire mata bututun ɗaukar ƙwai zuwa mahaifa ko kuma a kashe ta.
Ƴan bindiga sun kai wa ƴan sanda hari a Sokoto ‘sun kashe DPO’
A makon da ya gabata ne wasu ƴan bindiga suka kai hari a garin Gidan Madi da ke ƙaramar hukumar Tangaza a jihar Sokoto.
Maharan sun kai harin ne a ofishin ƴan sanda a tsakar dare kuma har sun kashe DPO a garin, kamar yadda wasu mazauna garin suka shaida wa BBC.
Wani mazaunin garin ya ce suna bacci suka ji ƙarar harbe-harben bindiga, wanda ya tayar da su daga bacci.
Rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta tabbatar wa BBC da harin, amma kakakin ƴan sandan jihar, ASP Muhammad Sadiq bai yi ƙarin haske ba musamman game da kashe DPO da ƴan bindigar suka yi ba.
Baya ga kashe DPO, mazauna garin sun kuma ce ƴan bindigar sun yi awon gaba da wasu mata a garin na Gidan Madi.
Buhari ya amince da sauya fasalin aikin ‘yan sanda a Najeriya
Asalin hoton, Nigeria Presidency
A ranar Alhamis din da ta gabata ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rattaɓa hannu a dokar kawo sauye-sauye ga aikin ‘yan sanda a ƙasar.
Dokar ta tanadi yadda rundunar ‘yan sandan za ta kasance mai ƙarin nagarta da kuma kyakkyawan tsari a aikinta, bisa manufofi na tabbatar da gaskiya da rikon amana a tafiyar da lamuranta da albarkatunta.
Dokar kuma ta tanadi wani tsari na musamman da rundunar za ta rinƙa samun tallafin kuɗi kamar yadda wasu manyan cibiyoyin gwamnati suke samu, haka kuma za a ƙara inganta aikin ta hanyar horo na musamman da za a rinƙa ba jami’an.
Aikin ‘yan sanda a Najeriya na daga cikin ayyukan da suka yi ƙaurin suna ta fannin cin hanci da rashawa, kuma ana zargin hakan ya samo asali ne sakamakon rashin kyakkyawan tsari da aka ɗora aikin tun a farko.
Gwamnatin Buhari ta bai wa ƴan Najeriya haƙuri kan kuskuren bayanin cike sabon fom na banki
Asalin hoton, BUHARI SALLAU
A makon da ya gabata ne Gwamnatin Najeriya ta nemi afuwar ƴan kasar kan wani sabon fom ɗin banki da ta fitar kuma ta bukaci su shiga bankunansu su cike.
Gwamnatin ta ce akwai kura-kurai a kan bayanin da tsarin cike fom din don haka ta goge sakon da ta wallafa na neman bukatar cike wannan fom din.
A ranar Alhamis ne gwamnatin Najeriyar ta wallafa sanarwar a shafinta na Tuwita inda ta buƙaci ƴan ƙasar da su shiga bankunansu su cike wani sabon fom.
Sannan masu amfani da banki fiye da ɗaya dole sai sun shiga bankunan sun cike sabon fom ɗin. Tsarin kuma ya shafi duk wani mai asusu a banki da suka haɗa da kamfanonin.