Mota ta faɗo daga kan gada ta kashe wata mace a Lagos

Wata mata dake tafiya akan babur ta mutu a Lagos bayan da wata mota ta faɗo daga kan gada akan babur ɗin da take kai.

Sola Giwa mai bawa gwamnan jihar Legas shawara kan harkokin sufuri ya ce motar ta ƙwacewa direban lokacin da yake ƙoƙarin kwana da ita yana tsaka da gudu.

Hakan ya sa motar ta faɗo kan babur ɗin daga kan gadar Iganmu.

Giwa ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 06:15 na safiyar ranar Litinin kuma direban ya gudu nan take saboda gudun kada fusatattun mutane sun farmasa.

Ya ƙara da cewa tuni aka ɗauke gawar matar ya zuwa asibiti aka kuma ɗauke motar kwantenar domin ababen hawa su samu sauƙin zirga-zirga.

More News

An gano gawarwakin ƴan fashin daji 8 a Kaduna

Gawarwaki 8 da ake zargin na ƴan fashin daji ne aka gano bayan da sojoji suka kai farmaki dazukan dake ƙauyen Kurutu dake kusa...

Tinubu ya karɓi Anyim Pius a jam’iyar APC

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya yi wa  tsohon shugaban majalisar dattawa,Anyim Pius Anyim maraba da zuwa  jam'iyar APC. A makon daya gabata ne Anyim...

Akpabio ya bawa Natasha Akpoti hakuri

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bawa Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi haƙuri kan furucin da ya yi mata akan gidan rawar...

Akpabio ya bawa Natasha Akpoti hakuri

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bawa Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi haƙuri kan furucin da ya yi mata akan gidan rawar...