Miyetti Allah ta nemi a cafke Sunday Igboho saboda barazanar yaƙar Fulani

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, ta yi kira da a damke wani dan kabilar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, bisa zargin yi wa Fulani barazana a wani faifan bidiyo.

A ranar Litinin, dan a-waren ya shaida wa magoya bayansa cewa kada su jira gwamnatin kasar kafin ta dauki matakin yaki da Fulani makiyaya, wadanda ya yi zargin suna hana manoman yankin shiga gonakinsu a yankin Kudu maso Yamma.

“Wannan yanki ne namu. Mu kubutar da kanmu daga hannun Fulani. Ya kamata mu sanya tsaro a duk ƙasar Yarbawa. Ba mu buƙatar jiran kowa, har da gwamnati. Idan da gaske muke yi , bai kamata mu jira gwamnati ba, in ba haka ba Fulani za su ƙwace filayenmu gaba daya. Ya kamata mu kasance da haɗin kai. Wadanne gonaki ne muke da su kuma a kasar Yarbawa?  Za mu iya zuwa gona a yanzu?”, Mista Igboho ya ce.

Da yake mayar da martani ga sanarwar, shugaban kungiyar ta MACBAN na kasa, Baba Othman Ngelzarma, ya yi kira da a kama Mista Igboho tare da gurfanar da shi a gaban kuliya saboda ya yi “kalamai na cin amanar ƙasa.”

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya ƙirƙiri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a ƙara wa ƴan bautar ƙasa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...