Ministan tsaron ƙasar Laberiya, Yarima Charles Johnson ma III, ya yi murabus daga muƙaminsa, biyo bayan zanga-zangar da matan sojojin kasar suka yi, saboda ƙarancin albashin mazajensu da kuma rashin rayuwa mai kyau a barikin soji.
Matan sun kafa shingaye a kusa da Monrovia babban birnin kasar da kuma wasu wurare, lamarin da ya tilasta wa shugaban ƙasar Joseph Boakai soke bikin ranar sojojin kasar da za a yi ranar Litinin.
Sun buƙaci ministan tsaron ya yi murabus, suna masu zarginsa da rage albashin sojojin Laberiya da suka dawo daga aikin wanzar da zaman lafiya a Mali.
Matan jami’an sun kuma yi tir da rashin tsaro na zamantakewa, karancin wutar lantarki da kuma almundahana a cikin rundunar.
An fara zanga-zangar ne dai a ranar Lahadi a kusa da barikin Edward Binyah Kesselly, a Monrovia.
Mista Johnson, a cikin wata sanarwa, ya ce ya yi murabus ne saboda “rikicin siyasa da na jama’a” da zanga-zangar ta haifar.
Sai dai ya musanta zargin yin amfani da kuɗaɗen soji, inda ya ƙara da cewa burinsa shi ne ya tabbatar da an wanzar da ɗa’a a cikin rundunar.