Ministan Tsaro, Mohammed Abubakar Badaru, ya jinjina wa Gwamna Dauda Lawal bisa jajircewarsa da ci gaba da tallafa wa ayyukan soji a Jihar Zamfara.
Ministan ya yi wannan furuci ne a ranar Alhamis lokacin da ya kai wa gwamnan ziyara a fadar gwamnatin Jihar Zamfara. Ya kuma ziyarci hedikwatar hadin gwiwar rundunar Fansar Yamma da ke Gusau, inda ya umarci dakarun da su kama fitaccen dan ta’adda, Bello Turji.
Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa manufar ziyarar ministan ita ce inganta hadin kai tsakanin gwamnatin jihar da ma’aikatar tsaro.
Sanarwar ta kara da cewa an tattauna batutuwan da suka shafi tsaro tsakanin ministan da gwamnan a matsayin ci gaba da taron da aka yi a farkon makon nan tsakanin Mr Badaru da Mr Lawal tare da takwaransa na Jihar Katsina, Dikko Radda, a ma’aikatar tsaro da ke Abuja.