Ministan lafiya ya ziyarci Duduwale

[ad_1]
Ministan lafiya Farfesa Isaac Adewale ya ziyarci, Abubakar Duduwale mutumin da ya yi tattaki daga Yola zuwa Abuja domin halartar bikin rantsar da shugaban kasa Muhammad Buhari a shekarar 2015.

Adewale ya ziyarci Duduwale wanda yanzu haka yake jiya a Cibiyar Kula Da Lafiya ta Tarayya dake Yola babban birnin jihar Adamawa, sakamakon ciwon kafa da yake fama da shi.

Ya yi alkawarin tabbatar da cewa Duduwale ya samu cikakkiyar lafiya.

Ministan ya sanar da haka cikin wani sakon Twitter da wallafa ɗauke da hoton Duduwale.

“Na ziyarci Abubakar Duduwale mutumin da yayi tattaki daga Yola zuwa Abuja don halartar bikin rantsar da shugaban kasa Muhammad Buhari a shekarar 2015 amma yanzu yana fama da jiyar rauni a kafarsa a Cibiyar Kula Da Lafiya ta Tarayya dake Yola.Zamu tabbatar da ya samu lafiya.”
[ad_2]

More News

Wani dan ta’adda ya faɗa hannun ƴan sanda a Yobe

Rundunar ƴan sandan jihar Yobe ta sanar da kama Haruna Muhammad mai shekaru 40 wanda aka yi ittifakin cewa shi ne shugaban wasu gungun...

Wani mahajjacin Jihar Filato ya riga mu gidan gaskiya a Makka

Allah ya yi wa wani mahajjacin jihar Filato Ismaila Musa rasuwa a birnin Makka na kasar Saudiyya.Daiyabu Dauda, babban sakataren hukumar jin dadin alhazai...

NAFDAC ta ce kar ƴan Najeriya su riƙa cin abincin da ya wuce kwana 3 a firij

Darakta Janar ta Hukumar NAFDAC, Farfesa Moji Adeyeye, ta bukaci ‘yan Najeriya da su guji ajiye dafaffen abinci a cikin firiji sama da kwanaki...

Ƴanbindiga sun kashe mutane a Jihar Kaduna

An tabbatar da mutuwar mutane shida yayin da wasu da dama tare da yin garkuwa da su a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka...