Millennials: Mece ce matsalar matasa na zamanin nan?—BBCNews

  • Paula Adamo Idoeta
  • BBC News Brazil
Millennials holding mobile phones

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Suna cike da buri nasu na kansu mai tarin yawa

Su ne wadanda aka haifa a zamanin da aka fara amfani da na’urori masu kwakwalwa, da wayoyin tafi-da-gidanka, da intanet da kuma samun labarai kamar saukar ruwan sama kan abubuwan da ke faruwa a duniya tun suna da kananan shekaru.

Suna cike da buri nasu na kansu mai tarin yawa: a yayin da kuma karin shekaru na karatu da ya danganci iyayensu da kuma yanayin zamantakewa daban-daban, da shekaru masu yawa na samun ilimi, da abubuwa, ‘mellenials’ (wadanda aka haifa tsakanin shekarun 1981 da 1996) na fatan samun karin ci gaba da kuma cin gajiyar abubuwan da duniya ta zo da su fiye da sauran ‘yan sauran zamanin.

Amma kuma, binciken kasashen duniya ya nuna cewa irin wadanda suka fada cikin wannan zamani, a zahiri akwai yiwuwar za su kasance cikin kangin basussuka fiye da kaka da kakanninsu kana za su dauki tsawon lokaci kafin su bar gidajen iyayensu ko kai wa ga irin nasarorin rayuwar zama baligai kamar sayen gidaje da filaye ko mota.

Wannan rashin alaka da ke tsakanin buri da kuma ainihin zahiri ya saka ‘ya’yan zamanin kasancewa cikin fuskantar zolaya da kalaman cin mutunci a shafukan sada zumunta game da ”gazawa”, da ”lalaci” da kuma yawan dogaro da iyayensu.

Abu mafi muni kuma shi ne, yanzu haka sukan fuskanci kallon hadarin-kaji daga generation Z wato (wadanda aka haifa daga tsakanin shekaru 1996 da 1998 ko 2000 zuwa yanzu) da yawanci suke yi wa ‘millennials’ ko ‘generation Y’ kallon ”wadanda ba su waye ba”.

Shin mene ne aibun “millennials” – kuma shin da gaske sun gaza?

‘Dora musu laifi rashin adalci ne’

Amsoshi daga masu bincike su ne, da farkon fari, wannan laifi ba a kan ainihi ‘yan wannan zamani na ‘millennials’ yake ba.

Asalin hoton, Getty Images

“Millennials sun girma a farkon lokacin da aka fara amfani da wayoyin tafi-da-gidanka da kuma intanet,” Jason Dorsey, shugaban Cibiyar Generational Kinecticism ( kamfanin da ke gudanar da bincike kan halayyar ”millennials da kuma generation Z), ya shaida wa BBC.

“Don haka, za a iya cewa sun zo a wuri da kuma daidai lokacin da ya dace za su samu gagarumin ilimi da tunanin abubuwa game da rawar matsayinsu da kuma irin rawa da za su taka a duniya.”

“Iyayensu sun shaida musu cewa za su kai ga nasara, suna da babbar dama ta samun ilimi idan aka kwatanta da ‘yan zamanin baya, kuma akwai alamun gagarumar alaka da tasiri game da hakan.”

‘Yan zamanin da suka fi rashin sa’a a tarihi’

Amma Dorsey ta bayyana cewa dole su fuskanci gagarumin koma-baya kamar durkushewar tattalin arzikin da ya biyo bayan matsalolin kudi daga shekarar 2008 zuwa 2009 da karin matsalolin da annobar korona ta haifar a baya-bayan nan.

“A hanyoyi da dama, an tsara wa musu yadda za su kai ga cimma nasara, amma sun ci karo da wasu matsaloli na durkushewar tattalin arziki, da rashin aikin yi, da hauhawar farashin kaya, da tsadar rayuwa,” in ji Dorsey.

Masanan sun kafa hujjojinsu da wasu bayanan kididdiga da suka tattara.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
“Millennials sun girma a farkon lokacin da aka fara amfani da wayoyin tafi-da-gidanka da kuma intanet

A Amurka, makalar da jaridar Washington Post ta wallafa a watan Yunin shekarar 2020 ta yi wa ‘yayan zamanin lakabi da “millennials su ne ‘yan zamani da suka fi rashin sa’a a tarihin Amurka”.

“Idan aka yi la’akari da matsalolin da ake ciki a yanzu na annobar korona, ‘yayan zamanin sun shaida tafiyar koma bayan tattalin arziki tun bayan da suka fara aiki fiye da ‘yan sauran zamani a tarihin kasar,” a cikin makalar.

“Millennials za su ci gaba da kasancewa da tabon kangin tattalin arziki na wannan har iya tsawon rayuwarsu, ta fuskar karancin samun kudaden shiga, karancin samun ci gaba da kuma tafiyar hawainiya wajen kai wa ga nasarorin rayuwa kamar na mallakar gida.”

Cigaba bangaren ko wannensu

Ko shakka babu, ko wane zamani ya fuskanci irin na shi kalubalen kuma abinda Dorsey ke kira da “lokuta na sauya tunani” – abubuwan da suka saka mutane fuskantar abubuwan da suka shige musu gaba, na fargabarsu, da zabinsu na ilimi da rayuwa, da dabi’u, da kuma fahimta game da makomarsu.

Ga misali “silent generation”- (wadanda aka haifa tsakanin shekarun 1928 da 1945) sun shaida Yakin Duniya na Biyu.

Su kuma ”Baby boomers” (mutanen da aka haifa tsakanin shekarun 1946 da 1964) sun shaida abubuwan da suka faru a duniya kamar Yakin Vietnam ko kuma zuwan dan adam duniyar wata.

Sai kuma ”Generation X” (wadanda aka haifa tsakanin shekarun 1965 da 1980), sun shaida karshen Yakin Cacar Baka da kuma yaduwar cutar HIV.

A yayin da su kuma ”Generation Z” (mutanen da aka haifa tsakanin shekarun 1997 da 2012), ko shakka babu sun shaida barkewar annobar korona.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
”Generation Z” (mutanen da aka haifa tsakanin shekarun 1997 da 2012), ko shakka babu sun shaida barkewar annobar korona.

Mutanen daukacin zamanin za kuma su fuskanci mummunan tasirin abubuwa kamar na abkuwar bala’oi, da annoba da kuma munanan tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa.

Shin menene ke ci wa ‘yan zamanin ‘millennial’ tuwo a kwarya?

Manyan abubuwa, in ji Jason Dorsey, su ne karuwar matsalolin tsadar rayuwa (musamman ilimi da mallakar gida a birane da dama a fadin duniya).

“Kafin zuwan mutanen zamanin da ake kira ‘generation Z’ ko kuma wadanda aka haifa a karnin baya-bayan nan, millennials sun fi yanayi da sauran ‘yan sauran zamanin a duniya, ya bayyana.

“Hakan na nufin mutane duka daya suke? A’a. Amma hakan na nufin suna da yanayi iri daya da dama, ta fuskar sadarwa, da nishadantarwa, da al’adu, da kuma shiga harkokin siyasa.”

“Dangantakar tattalin arziki ta fi kulluwa, kamar a bangaren tsarin bankuna da kamfanoni.

“Kana idan muka duba bangaren ayyukan yi, akasarin kamfanonin na da rassa a kasashe daban-daban ne.”

“Mutanen zamanin na jin suna da alaka wacce babu ita a baya,” in ji kwararren.

Dorsey ya bayyana cewa ‘millennials’ sun waye da sanin abubuwan da ke faruwa a kasashen duniya saboda samun bayanai daga yanar gizo da ke saka abubuwan da suka faru a yanki daya ya yadu a fadin duniya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Millennials suna fama da matsalolin tsadar rayuwa

“Ba ina magana a kan abubuwan da suka faru kamar yakin duniya ba, amma batun cewa matsalolin bankuna a kasa daya ka iya yin gagarumin tasiri kan sauran mutane tare da yaduwa a fadin duniya.”

“Wannan abu ne mai matukar muhimmanci.”

Karfin mutanen zamani na millennials

Amma ba duka abubuwa ne suka kasance marasa dadi ga millennials ba.

Bincike yan una cewa sun fi wayewa da sanin abubuwan da ke gabansu masu amfani fiye da sauran wadanda aka haifa a zamanin baya.

Misali, ‘yan zamani ne na farko da suka dauki mataki kan rashin nuna daidaiton jinsi a bangaren biyan albashi da daukar ma’aikata.

Duk da cewa kwararru irin su Dorsey sun yi amanna akwai yiwuwar sauye-sauye masu karfi daga generation Z wato wadanda aka haifa a karnin baya-bayan nan.

Har ila yau su kuma millennials na mutunta harkar kasuwanci – fiye da iyayensu ko kakanninsu.

“Millennials sun zama balagai a daidai lokacin da amfani da intanet ya kara wa ‘yan kasuwa kaimi,” in ji Dorsey.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Millennials suna kuma fama da matsalolin rashin aikin yi

“Har ila yau, millennials za su iya gudanar da harkar kasuwancinsu ta shafin intanet, cikin sauki. Amma kuma, abinda muka shaida shi ne akasarinsu sun fara kasuwanci da aikinsu ne (a matsayin hanyar karin samun kudaden shiga).”

“Millennials suna basira, galibi matasa ne kuma za su amfana da duk abinda farfadowar tattalin arziki ya zo da shi nan da shekaru masu zuwa,” in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images

“Suna da isasshen lokaci a gaban su da zai ba su damar yanke shawarar game da abubuwan da za su amfane su.”

“Ta wani gefen kuma, millennials bas u taki sa’a ba, saboda ta wani bangaren, har yanzu suna da lokacin da za su amfani da shi,” in ji Dorsey.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Duk da rashin dacen da suka yi, amma suna da dama ta fannin tattalin arziki, in ji Dorsey

Ya kuma kara da cewa: “Amma kuma, mun kawo karshen mutanen zamanin millennial a shekarar 1995 saboda harin 9/11, wanda yana da matukar muhimmanci a yankuna da dama na duniya.

Kuma wadanda aka haifa bayan shekarar 1995 ba sa iya tunawa da . 9/11,” ya bayyana.

Asalin hoton, Getty Images

More from this stream

Recomended