Messi da Neymar za su buga wa PSG karawa da Club Brugge

Neymar Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

Lionel Messi da Neymar suna cikin ‘yan wasan Paris St Germain da za su kara da Club Brugge a Champions League ranar Laraba.

PSG za ta ziyarci Belgium, domin fafatawa da kungiyar Belgium a wasan farko na cikin rukuni na daya a gasar ta zakarun Turai ta bana.

‘Yan wasan biyu ba su yi wa PSG wasan gasar Ligue 1 ranar Asabar da ta doke Clemont 4-0 ba.

Messi da Neymar sun buga wa kasashensu wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya ranar Alhamis, sannan suka koma birnin Paris a daren Juma’a.

Angel Di Maria dan kwallon tawagar Argentina ba zai yi wa PSG wasan Champions League uku ba a bana, bayan da UEFA ta dakatar da shi, sakamakon ketar da ya yi wa Fernandinho a bara a fafatawa da Manchester City karawar daf da karshe.

Har yanzu Sergio Ramos bai fara buga wa PSG wasa ba, tun bayan da ya koma kungiyar daga Real Madrid a bana, wadda ta kasa cimma yarjejeniyar tsawaita kwantiragin mai tsaron bayan, wanda ke jinya kawo yanzu.

Shima Marco Verratti baya cikin ‘yan kwallon da za su buga wa PSG karawa da Club Brugge, bayan da ya yi rauni a lokacin da ya yi wa tawagar Italiya wasan nemna gurbin shiga gasar cin kofin duniya.

(BBC Hausa)

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...